Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Sheikh Ikramah Sabri Limamin Juma'a a masallacin Aqsa ya mayar da martani kan hukuncin kotun Isra'ila da ya halastawa yahudawa yin ayyukansu na ibada a cikin wannan masallaci, inda ya ce kotun Isra'ila ba ta da wannan hurumi.
Ya ci gaba da cewa, wannan hukunci na kotun Isra'ila da ya bai wa yahudawa damar yin abin da suka ga dama cikin masallacin Quds da sunan ibada ko raya wasu abubuwa na addini, yin hakan shi kansa wani nau'in shisshigi ne akan wannan masallaci.
Kuma a cewarsa, wannan wani shiri ne daga shirye-shiryen da yahudawan suke da shi na kwace iko da wanann masallaci, tare da mayar da shi wurin harkokinsu, da kuma haramta wa musulmi yin ibada a cikinsa, wanda kuma a cewar malamin ba za su amince da hakan ba matukar dai suan a raye.
Su ma a nasu bangaren kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa da suka hada da Hamas da kuma Jihadul Islami, sun bayyana hukuncin da cewa, yunkuri ne na neman halasta ayyukan wuce gona da iri, wanda yahudawa suke yi a kan kaddarorin musulmi a birnin Quds, daga ciki har da masallaci mai alfarma.
342/